Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA reshen Jihar Jigawa ta ce tayi nasarar kama mutane 134 bisa kamu su da laifin yin hulda da kwayoyi wanda kudaden su ya kai Miliyoyin Nairori cikin makonni 2 da suka gabata.

Da take gabatar da masu laifin da aka kama ga manema labarai Kwamandan hukumar ta Jihar Jigawa Malama Maryam Gambo Sani, ta ce an kama mutanen ne, biyo bayan sumamen da suka gudanar a ranakun 27 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Octoba.

A cewarta, a lokacin sumamen sunyi nasarar gano mashayar mutanen da dama.

Haka kuma ta ce kaso 99 cikin 100 na mutanen da ake zargin, suna amfani da kwayoyi ne, kuma suna cigaba da bawa hukumar bayanan sirri kan mutanen da suke sayar musu da kwayoyin.

Hajiya Maryam Gambo, ta ce daga cikin wadanda suka kama, 132 Maza ne, sai kuma 2 Mata, da wasu 2 masu sarautun gargajiya, tare da Ma’aikatan gwamnati 2.

Kazalika, ta ce sun yi nasarar kama Daliban Makarantun gaba da sikandire su 25 na Jihar nan a lokacin kamen.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: