A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta ce ta cafke mutane 14 da ake zargi da laifi a kananan hukumomin Gumel da Kazaure.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da kamen ga Kamfanin Dillancin Labarai na kasa a birnin Dutse.

Shiisu Adam ya ce an kai samamen ne a wasu sanannun wuraren aikata laifuka da maboyar masu laifi inda aka cafke wadanda ake zargi.

Mai magana da yawun rundunar ya nakalto kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Sale, yana shawartar masu aikata laifuka da su gyara halayyarsu ko barin jiharnan.

Ya ce Kwamishinan ‘yan sandan ya yi alkawarin kai hare-hare akai-akai kan maboyar masu aikata miyagun laifuka da wuraren aikata badala a duk fadin jihar don fatattakar masu aikata miyagun laifuka.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: