Bola Tinubu ya shawarci sojojin da ke mulki a Nijar, su mayar da ƙasar kan turbar dimokraɗiyya a cikin wata 9

0 299

Jagoran ƙungiyar Ecowas kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shawarci sojojin da ke mulki a Nijar, su mayar da ƙasar kan turbar dimokraɗiyya a cikin wata tara, kamar yadda Najeriya ta yi a shekarun 1990.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS ta kakawa Jamhuriyar Nijar takunkumai tun baya da sojoji suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohemed Bazoum,tare da bazanar yin amfani da karfi soji domin dawo da mulkin farar hula a kasar.

Jagarorin juyin Mulki a Nijar sun daga cewa sai nan da shekaru zasu maida mulki ga farar hula a kasar tare da dawo da tsoffin dokokin kasar,sannan kuma gwamnatin sojin kasar ta baiwa yan sandar kasar umarnin tisa keyar Jakadan kasar Faransa dake Nijar din.

Shugaba Tinubu yace shekarun 1999 an dawo mulkin farar hula a Najeriya lokacin gwamnatin soji ta Janar Abdulsalami Abubakar, wanda yanzu shine mai shiga tsakanin sojin Nijar da kungiyar ECOWAS. Shugaba Tinubu ya kuma ce kungiyar ECOWAS bazata janye takunkuman da ta sanyawa Nijar ba har sai sun maida mulkin farar hula a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: