Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a fitar da kudade domin a fara biyan albashin ma’aikata 774,000 da aka dauka domin gudanar da wasu ayyuka na musamman a yankunansu.

Minista a Ma’aikatar Kwadago da Samar da Ayyukan yi, Festus Keyamo ne ya sanar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar.

Ministan ya kuma ce tuni ya umarci Hukumar Samar da Ayyuka ta Kasa (NDE) da ta shirya biyan kudaden ma’aikatan a Kananan Hukumomi 774 na Najeriya.

A watan Janairun wannan shekar nan ne dai Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin wanda zai samarwa da matasa 1,000 da ayyukan yi daga dukkan Kananan Hukumomin Najeriya 774.

A cikin shirin dai, an tsara za a rika biyan kowannensu N20,000 har na tsawon watanni uku masu zuwa.

Minista Keyamo ya ce za a rika biyan matasan ne ta asusun ajiyarsu na bankuna da suka bayar yayin rijista.

Sai dai ya ce za a yi amfani ne da Lambar Tantancewarsu ta Banki ta BVN domin kaucewa almundahana a yayin biyan.

Sai dai ya ce dukkan wadanda suka yi rijista da wasu sunayen na daban ba za su sami ko sisin kwabo ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: