Zaben shugaban kasa a Kongo Brazzaville

0 87

‘Yan Kongo Brazzaville na zaben shugaban kasa da babbar jam’iyyar adawa ta kaurace wa, zaben da ake ganin shugaba Denis Sassou Nguesso zai lashe.

Ana saran mai shekaru 77 da haihuwar ya lashe zaben da yake takara da wasu mutane shida, karkashin jagorancin masanin tattalin arziki kuma dan takarar shugaban kasar a shekara ta 2016 Guy-Brice Parfait Kolelas, wanda a jiya ya sanar da cewar, yana cikin rashin lafiya mai tsanani.

Tun a shekara ta 1979 ne dai Sassou Nguesso ya haye karagar mulkin Kongo, shekaru 36 a kan karaga ya sa shi zama daya daga cikin shugabnnin masu salon mulki na sai madi ka ture.

Ya na saran zarcewa a kan mukamin nasa na shugabancin wannan kasa ta tsakiyar Afirka mai azrikin man petur a karo na hudu, ba tare da wani tantama ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: