Buhari Ya Halaarci Taron Shugabannin Kasashen Dake Gabar Tekun Guinea Na Karshe A Matsayin Shugaban Kasa

0 80

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya a birnin Accra na kasar Ghana, ya bayyana cewa gudanar da tarurruka akai-akai tsakanin kasashen da suka hada da gabar tekun Guinea a matsayin wata muhimmiyar hanya ta samar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugaban kasar na magana ne a karo na karshe a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya a wani zama na musamman na majalisar shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen yankin gabar tekun Guinea, da ke gudana a babban birnin na kasar Ghana.

Yayin da yake nanata kudurin Najeriya da matakan yaki da matsalar rashin tsaro a gabar tekun Guinea, shugaba Buhari ya karfafa gwiwar kasashen mambobin kungiyar da su kafa dokokin yaki da fashin teku da sauran laifuka kamar yadda Najeriya ta yi.

Ya yi karin haske kan matakan da kasar ta dauka zuwa yanzu domin kara nuna tsayin daka kan farfado da karfafa hukumar kula da gabar tekun Guinea domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: