Ana Kyautata Zaton Kasar Najeriya Zata Kashe $2.8Bn Saboda Zazzabin Cizon Sauro

0 160

Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya ce matsalar zazzabin cizon sauro a Najeriya na iya kara dorawa kasar nauyin kudade kimanin dala biliyan 2 da dubu 800 nan da shekarar 2030.

Da yake jawabi jiya a Abuja yayin bikin tunawa da ranar zazzabin cizon sauro ta duniya ta bana, ya ce nauyin kudaden da cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya a shekarar 2022 kadai an kiyasta ya kai dala biliyan 1 da dubu 600.

Ministan, wanda babban sakataren ma’aikatar, Mamman Mamuda, ya wakilta, ya ce an kiyasta cewa kimanin mutane miliyan 55 ne ke kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da kuma mutuwar mutane kimanin dubu 90 a duk shekara a Najeriya.

Ya ce an kiyasta cewa kaso 70 cikin 100 na ‘yan Najeriya na kashe kusa naira dubu 2 da 280 daga aljihunsu saboda maganin cutar malaria. Ya ce nasarar shawo kan cutar zazzabin cizon sauro zai kara kwarin gwiwar aiki, da inganta kiwon lafiya, da rage rashin zuwa makaranta, da rage talauci da saukaka cimma muradun ci gaba mai dorewa.

Leave a Reply