Ma’aikatan Wucin Gadin Hukumar Kidaya Fiye Da 300 Ne Sukayi Zanga-Zanga A Kano Kan Rashin Biyan Su Alawus-alawus

0 80

Sama da ma’aikatan wucin gadi 300 na Hukumar Kidaya ta Kasa a Kano sun yi zanga-zanga kan rashin biyansu alawus-alawus na horo na kwanaki 18 tun daga watan Fabrairun 2023.

Mai magana da yawun ma’aikatan, Aliyu Rulwanu ya zargi hukumar da tsarin biyan kudi wanda a cewarsa ya sabawa sharuddan da aka cimma.

Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a na hukumar ta Kano, Jamila Abdulkadir Sulaiman, ta bayyana cewa ma’aikatan sun tafka kura-kurai wajen cike fom kuma hukumar na daukar lokaci domin gyara su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: