CBN ya bayyana kudurinsa na sayar da Baitulmalin Naira Biliyan 722 daga cikin kudaden Ajiya

0 126

Babban Bankin Kasa CBN ya bayyana kudurinsa na sayar Baitulmalin Naira Biliyan 722 daga cikin kudaden Ajiya nan da watan 9 na wannan shekara.

Bankin ya bayyana hakan ne, cikin wani shirin baitulmatin da bankin ya shirya karo na 3 cikin shekarar 2021 da muke ciki.

Shirin wani kuduri ne na CBN wanda hakan zai bashi damar ciyowa bashi daga kudaden Ajiyar mutane, a madadin gwamnatin tarayya.

Jadawalin shirin yayi nuni da cewa CBN zai sayar da Naira Biliyan 106.1 a cikin watan Yuni sai kuma Naira Biliyan 7.26 nan da kwanaki 91 da kuma Naira Biliyan 9.52 nan da kwanaki 182, yayin da kuma zai sayar da Naira Biliyan 89.32 cikin kwanaki 364.

Leave a Reply

%d bloggers like this: