Kungiyar Malaman Jami’oi (ASUU) ta sake barazanar tafiya yajin aiki

0 99

Kungiyar Malama Jami’oi ta Najeriya tayi barazanar tafiya yajin aiki, matukar ba’a biya Malamai dubu 1,000 Albashin Watanni 13 ba.

Shugaban Kungiyar na Kasa reshen Jami’ar Jos ta jihar Plateau Dr Lazaras Maigoro, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Jos, inda ya kara da cewa kawo yanzu Gwamnatin tarayya bata biya Malaman Albashin su ba.

Haka kuma, ya kalubalanci Babban Akawu na Kasa Ahmed Idris, bisa yadda ya kyale Mambobin na mutuwa saboda rashin biyansu hakkin su, duk da cewa Kungiyar ta cimma yarjejeniya tsakaninta da gwamnatin tarayya bayan yajin aikin da suka gudanar a baya.

Shugaban Kungiyar, ya ce, ana yiwa Mambobin su barazanar su shiga tsarin nan na IPPS ko kuma a rike Albashin su.

Dr Maigoro, ya ce duk da umarnin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayar na biyan Mambobin na su hakkokin su, Babban Akawu na Kasa ya hana Malaman hakkokin su, wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar da aka yi tsakanin Kungiyar da Gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: