Cibiyar NCDC ta ce kimanin sabbin mutane 268 ne suka harbu da cutar Corona a Najeriya

0 72

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce kimanin sabbin mutane 268 ne suka harbu da cutar Corona a Kasar nan cikin Jihohi 10 da ake dasu.

NCDC ta ce a jiya an samu mutane 225 da suke dauke da cutar a Jihar Lagos, sai Rivers 17 da Enugu 10.

Sauran Jihohin sune Edo (5), Bauchi (3), Ogun (3), Oyo (2), sai kuma Kaduna, Bayelsa da kuma Delta mai mutane dai-dai.

Haka kuma hukumar NCDC ta ce an sallami mutane 25 daga Cibiyoyin kula da masu cutar a kasar nan bayan sun warke.

Kawo yanzu adadin mutanen da cutar ta hallaka sun kai dubu 2,980 a kasar nan baki daya tun bayan bayyanarta.

Kazalika, daga watan Fabreru na shekarar 2020, zuwa yanzu kimanin mutane dubu 215,164 ne cutar ta kama, inda aka samu mutane dubu 207,520 da suka warke daga cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: