Manyan ayyukan da shugaba Buhari zai ƙaddamar a Legas

0 180

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa Legas babban birnin kasuwanci na Kasar nan domin ƙaddamar da wasu ayyuka a yau.

Rahotanni na cewa cikin ayyukan da zai ƙaddamar sun hada da wasu sabbin Jiragen ruwa na yaƙi a tashar ruwa ta sojin ruwan ƙasa da ke Victoria Island.

Tuni hukumar kiyaye haɗura ta jihar Legas LASTMA ta ba Jama’a shawara da su kiyayi da bi ta titin Ahmadu Bello sakamakon ziyarar shugaban.

An bayar da rahoton cewa tuni sojoji da ƴan sanda da jami’an DSS suka cika unguwar Victoria Island wanda nan ne shugaba Buhari zai je.

Ana kuma sa ran Shugaban Kasar bayan ƙaddamar da ayyukan zai halarci  bikin ƙaddamar da wani littafi wanda tsohon Shugaban Jam’iyar APC Chief Bisi Akande ya rubuta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: