Mazauna wasu ƙauyuka a jihar Filato sun bayyana damuwa kan ayyukan masu garkuwa da mutane a yankin

0 155

Mazauna wasu Kyauyikan Sapiyo da Bangala dake Karamar Hukumar Wase ta Jihar Plateau sun bayyana damuwa kan ayyukan masu Garkuwa da mutane a yankin, inda suka bukaci tallafin Jami’an tsaro.

Kyauyawan sun ce masu Garkuwa da mutanen suna gudanar da ayyukan su a kullum tare da bindigogi.

Shugaban Matasan Wase, Malam Shafi’i Sambo Haruna, ya fadawa manema labarai cewa hare-haren da masu Garkuwa da mutane suke kaiwa Kyauyawan ya dakatar da kasuwanci a yankin tare da jefa su cikin kunci.

A cewarsa, yan bindigar suna hana yan kasuwa zuwa wurin kasuwancin su na yau da kullum, wanda hakan ne yasa Jami’an tsaro da yan bijilanti zuwa maboyar yan bindigar amma sai suka gudu.

Malam Shafi’i ya bukaci masu sarautun gargajiya da sauran mutanen yankin su tallafawa Jama’a domin dawo da zaman lafiya a karamar hukumar ta Wase.

Leave a Reply

%d bloggers like this: