Gwamnatin Jihar Kaduna ta fara shirya wa malaman firamare na Jihar jarrabawar auna ƙwarewarsu

0 198

Gwamnatin Jihar Kaduna ta fara shirya wa malaman firamare na Jihar Jarrabawar auna ƙwarewarsu da zummar inganta aikin koyarwa.

Hakan na zuwa ne kusan shekara huɗu bayan malaman sun rubuta irin wannan jarrabawar da ta kai ga korar abokan aikinsu kusan 22,000 sannan aka ɗauki kusan 25,000 da gwamnati ta ce sun cancanta.

Da yake magana yayin ƙaddamar da Jarrabawar ta hanyar kwamfuta, shugaban hukumar ilimi a matakin farko ta Jihar Alhaji Tijjani Abdullahi ya ce ba don a kori malamai aka shirya gwajin ba.

A 2017 ne Ma’aikatar Ilimi ta Kaduna ta kori malaman makaranta fiye da 20,000 da ta ce sun gaza cin jarrabawar gwajin a lokacin.

Kungiyoyin Malaman Makaranta da na Kwadago sun kalubalanci shirya Jarabawar, inda suka bukaci a gudanar da zanga-zangar Lumana a lokacin.

A cewarsa, an shirya jarrabawar ne don a gano wuraren da ake da buƙatar yin gyara da kuma bai wa malaman horo.

Kazalika, ya ce malaman da suka zauna Jarrabawar za su ga sauyi kan yadda za a gudanar da ita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: