Dakataccen Shugaban Jam’iyar PDP na Kasa ya bukaci da ta dakatar da shirin taronta har sai kotu ta yanke hukunci

0 62

Dakataccen Shugaban Jam’iyar PDP na Kasa Prince Uche Secondus ya bukaci Jam’iyar ta dakatar da kudurin ta na shirya gangamin ta na kasa wanda zata shirya gudanarwa har zuwa lokacin da Kutun daukaka kara zata yanke hukunci.

Manema Labarai sun rawaito yadda wasu kutuna suka bawa Uche Secondus umarnin ya dakatar da shiga Ofishin Jam’iya, tare da nada Mista Yemi Akinwonmi, a matsayin wanda zai gajeshi a kujurar.

Cikin wata sanarwa da Lauyan sa Barista Tayo Oyetibo, ya fitar mai kwanan wata 21 ga watan Octobar da muke ciki, inda ya bukaci Jam’iyar ta mutunta umarnin Kotu har zuwa lokacin da za’a kammala sauraron karar da aka shigar.

A ranar 10 ga watan Satumba ne wata Kotu wanda take zamanta a Jihar Rivers ta yanke hukuncin dakatar da Prince Uche Secondus, daga kujerar shugaban Jam’iyar da kuma gabatar da kansa a matsayin shugaban Jam’iyar PDP na Kasa.

An rawaito cewa tuni Prince Secondus, ya daukaka kara kan dakatarwar da Kotun Jihar Rivers tayi masa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: