Dalilin gurfanar da Muhuyi Magaji a gaban kuliya

0 104

Hukumar da’ar ma’aikata ta bayyana dalilin da ya sa ta gurfanar da shugaban hukumar korafe-korafe da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji a gaban kuliya.

An gurfanar da Magaji a gaban kotun (CCT) bisa zargin cin hanci da rashawa 10.

An tattaro cewa Magaji zai bayyana a kotu a ranar 10 ga Janairu, 2024.

Manema labarai sun tattaro cewa an gurfanar da shugaban hukumar yaki da cin hanci na jihar Kano a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba, a kotun CCT.

A cewar shugabar, manema labarai da hulda da jama’a, Misis Veronica Kato, tace tuhumar da ake yiwa Muhuyi Magaji ta hada da saba ka’idojin da’a na jami’an gwamnati,  cin zarafin ofishi, bayyana kadarorin karya, cin hanci, karbar kyauta, da sauransu.

Bincike ya nuna cewa shugaban ya gaza kare wasu asusu na banki masu dauke da sunansa mai dauke da kudi naira miliyan 394 wanda hakan ya sa ake masa zargin almundahana.

Ta ce, duk da haka an bayar da belin wanda ake tuhuma da kudi Naira miliyan 5 tare da mutane biyu masu tsaya masa da suke da kadarori a cikin babban birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: