An kashe ‘yan ta’adda da dama a Tsaunin Doka da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna

0 234

Rundunar sojin sama ta ce ta kashe ‘yan ta’adda da dama a Tsauni Doka da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar labarai Air Commodore Edward Gabkwet ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Gabkwet ya ce rundunar Operation Whirl Punch ce ta kai harin.

A cewarsa, an kai harin ne bayan ango wasu sahihin bayanan sirri ce wa wani shugaban ‘yan ta’adda da aka fi sani da Boderi.

Ya ce an kai hare-hare ta sama a wurin da sanyin safiyar ranar alhamis , wanda ya haifar da mummunar illa ga ‘yan ta’addan. An zargi Boderi da dan uwansa Nasiru tare da ‘yan kungiyarsu da kai hare-hare da sace-sacen mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna, hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da kuma wasu al’ummomi a jihohin Neja da Kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: