Dan Majalisa Ya Bayarda Tallafin Fam Din Jamb Ga Dalibai 200 A Jigawa

0 169

An gabatar da taron tallafawa Dalibai 200 da fam din Jamb a karamar hukumar Hadejia, wanda dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Hadejia Barr. Abubakar Sadik Jallo ya kaddamar jiya, a garin Hadejia.


Taron yasamu halartar manyan mutane kamar su mai girma Baraden Hadejia Amb. Haruna Ginsau da Shugaban karamar Hukumar Hadejia Hon. Abdullahi Muhammad Mai Kanti da Sakataren karamar Hukuma Hon. Ahmad Hassan Yayari da Tsohon Shugaban Karamar Hukuma Hon. Abba Haruna Jindo (Ruwa Baba) da kuma daliban da suka amfana da tallafin.


A jawabin Shugaban Karamar Hukuma Hon. Abdullahi Muhammad Mai kanti ya nuna jindadi da wannan kuduri na dan majialisa don ganin ya gina Matasa, sannan ya kara jan hankalin sauran yan siyasa da masu hannu da shuni da suyi koyi da irin wannan abin alheri.

Tsohon Shugaban karamar Hukuma Hon Abba Haruna ya yaba da kokarin dan majalisar ya kara da cewa Allah ya karawa Hadejia irin wannan yan siyasa masu son gina matasa.


Shi ko mai girma Baraden Hadejia Amb. Haruna Ginsau ya gargadi matasan da su kiyaye mutuncinsu a duk inda suka sami kansu, kuma su jitsoran Allah su tsaya suyi karatu dan amfanin kansu da kasa baki daya.


Daga karshe an karkare taron bayan wasu daga cikin daliban sun karbi nasu fam din, wanda Shugaban Karamar Hukumar ya bayar da hannunsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: