Dan takarar gwamman jihar Jigawa a APC, Hon. Faruk Adamu Aliyu yayi fatali da tsarin sasanto domin gudanar da zaben fidda gwamni
Dan takarar gwamman jihar Jigawa a tutar Jam’iyyar APC Faruk Adamu Aliyu ya jaddada matsayarsa na tabbatar da gudanar da zaben fidda gwamni dan takarar gwamna a tutar jam’iyyar APC.
Tare da yin fatali da tsarin sasanto.
Faruk Adamu Aliyu ya bayyana hakan ne a yau Juma’a a birnin Dutse a lokacin dayake kaddamar da takararsa a gaban magoya bayansa.
Ya kuma bukaci gwamna Muhammad Badaru Abubaka dayaji tsoron Allah kuma ya zama mai Magana daya.
Kamar yanda a kwanakin baya yace, babu wani dan takarar dayake goyan bayan a cikin masu neman yiwa jam’iyyar Takara a zaben 2023.
Aliyu ya kuma bukaci gwamna Badaru daya amince a gudanar da zaben fidda gwani cikin gaskiya da adalci a tsakanin yan Takarar.
Ya kara da cewa dole ne a tabbatar da gaskiya da adalci a dukkanin zabukan fidda gwani da za’agudanar da fadin jihar nan.