Labarai

Ministan matasa da wasanni Sunday Dare, ya ce gwamnati ta kudiri aniyar amfani da wasanni wajen kawar da talauci a kasar

Ministan matasa da wasanni Sunday Dare, ya ce gwamnati ta kudiri aniyar amfani da wasanni wajen kawar da talauci a kasar.

Ya fadi haka ne jiya a Abuja a wajen taron Rotary karo na 13.

Ya ce ma’aikatar ta gabatar da wata sabuwar manufar wasanni ta kasa da za ta inganta harkokin wasanni da kuma kara zuba jari a fannin wasanni.

Yayin dayake gababatar da jawabinsa Gwamnan gundumar Ayoola Oyedokun, ya ce a karkashin sa, mambobin gundumar sa sun karu da fannin wasanni.

Ya kara da cewa hakan ya baiwa gundumar damar yiwa al’umma hidima a Najeriya.

Oyedokun ya ce, ya mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ga yara mata da kuma samar da ruwa mai tsafta da kuma tsaftar muhalli ga al’ummomin karkara, duk ta hanyar wasanni.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: