Darasin Korona: Gwamnatin Sokoto Zata Gina Babban Asibitin Koyarwa da Wasu Asibitocin Kwararru 2

0 200

A yau Majalisar Zartarwa ta jihar Sokoto wadda Gwamna jihar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ke jagoranta ta aminta da bada kwangilar gina wasu ayukka guda 3:

  1. Gina sabuwar asibitin koyarwa ta jami’ar jihar Sokoto akan kudi Naira Biliyan 6 da Naira Miliyan 606 wadda zaa kammala a cikin watanni 30. Wadda zaa gina a Kasarawa.
  2. Gina Sabuwar asibitin Kwararru Wato Premier Hospital a Sabon Birni akan kudi Naira Biliyan 1 da Miliyan 780 wadda zaa gina cikin watanni 17.
  3. Sai gina wata sabuwar asibitin ta Premier a Garin Tambuwal akan kudi Naira Biliyan 1 da Miliyan 767 wadda zaa gina a cikin watanni 18.
  4. Sai kuma amincewa da Asibitin Murtala ta cigaba da zaman ta na asibitin Kwararru ta jiha wadda zata zamo kari ga hukumomin lafiya da jihar sokoto take da su.

Kwamishinonin yada labarai Alh Isa Bajini Galadanci dana Kudi Alh. Abdulsamad Dasuki da na lafiya Dr. Ali Muhammad Inname sune suka yi ma manema labarai bayanin bayan taron na Majalisar.

Taron Majalisar Zartarwa ya samu halartar Shugaban ta Gwamna Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal da Mataimakin sa Hon. Manir Muhammad Dan’iya da Sauran membobin Majalisar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: