Gwanna Badaru Ya Bukaci Wadanda Suka Bude Makarantun Islamiyya da su Sake Rufewa

0 121

Hadakar kungiyar makarantun Islamiyya ta jihar Jigawa ta umarci dukkanin makarantun islamiyyaun da suka koma karatu dasu rufe, ba tare da bata lokaci ba.

Da yake bayarda umarnin a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a birnin Dutse, Ahugaban kungiyar Malam Aliyu Ibrahim Sakwaya yace hakan ya biyo bayan umarnin da mai girma gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayar a jawabinsa na musamman ga al’umar jihar.

Malam Sakwaya yace kungiyar makarantun Islamiyya mai biyayyace ga umarnin da gwamnati ta bayartare da jaddada cikakken goyan baya ga gwamnatin jiha da maikatan lafiya kan matakan da aka dauka na yaki da cutar covid19 a fadin jihar.

Shima a nasa jawabin sakataren kungiyar makarantun ya yi kira ga gwamnatin jiha data duba halin da ake ciki kasancewar watanni hudu kenan da rufe makarantun suna cikin damuwa sabida rashin biyan malamansu alawus da kudin hayar makarantun duba da halin da ake ciki na annobar corona virus.

Daga nan ya yabawa gwamnatin jihar jigawa bisa matakan da take dauka na dakile bazuwar cutar, inda yayi fatan jamaa zasu kalli lamarin da idon basira domin marawa gwamnati baya ta cimma wannan buri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: