Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sahalewa kudirin samar da cibiyoyin binciken magunguna, da bada horo a kwalejojin karatun likita 6 dake shiyyoyin kasarnan.
Bugu da kari Shugaba Buhari, ya amince da karin kudin hukumar na shekarar 2020 zuwa naira biliyan 7 da miliyan 5, sabanin naira biliyan 3 da yake a baya.
Babban sakataren hukumar TETfund, Farfesa Sulaiman Bogoro, shine ya bayyana hakan, yayin taron kwamatin amintattu na shekarar 2020 da aka gudanar a Abuja.
- Sanata Shehu Buba zai horas da matasa 250 kan sana’ar gyaran takalma a jihar Bauchi
- Cibiyoyin kula da lafiyar kafafu da hannaye a Najeriya ta bude sabon ofishi a Kano
- Gwamnan Namadi ya amince da Mai Martaba Sarkin Kazaure a matsayin Amirul Hajj na jihar Jigawa
- Dalibai 41,000 da ba su kai shekara 16 ba sun yi rajistar JAMB ta shekarar 2025
- Za a fara gudanar da jarrabawar WAEC da NECO ta hanyar na’ura wato CBT
Yace amincewa batun ya baiwa hukumar TETFund damar gina dakunan gwaje gwajen cutuka masu yaduwa biyu a kowacce shiyyar kasarnan, abinda zai sanya hukumar ta zama gagara misali, wajen samar da cibiyoyin gwajin cutar corona a Nigeria.
Farfesa Bogoro ya kuma ce kwamatin amintattun hukumar, ya amince da zuba naira miliyan 200, domin daukar nauyin wasu jami’o’i dama hukumar NAFDAC wajen gudanar da bincike kan cutar corona.