Dr. Yazid: Tafiyar Buhari Kasar Waje Barnar Kudin Kasa Ne

0 80

Masu sharhi sun fara kushe tafiyar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi zuwa Ingila domin duba lafiyarsa, matakin da suka bayyana a matsayin barnar kudin kasa.

un bayar sanarwar da mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari, shawara a harkokin watsa labarai Femi Adeshina ya fitar a jiya Litinin, wadda ke bayyana cewar shugaban zai yi balaguro zuwa kasar Burtaniya, don duba lafiyar shi kamar yadda ya saba, ‘yan Najeriya suka shiga caccakar fadar da yin allah wadai.

Da safiyar yau Talata ake sa ran shugaban na Nijeriya Muhammadu Buhari, zai kama hanya zuwa Ingila domin duba lafiyar sa na shekara-shekara da ya ke yi. Sanarwar ta kara da cewar shugaban zai dawo a tsakiyar watan Afrilu, amma kamun ya kama hanya a yau zai yi wata ganawa ta musamman da hafsoshin tsaron kasar.

Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu BuhariNigeria, da Najeriya.

A hirar shi da manema labarai, mai magana da yawun shugaban Garba Shehu, ya bayyana cewa “Ai wannan tafiyar ba sabuwar abu bace, dama sama da shekaru 30, yakan yi irin wannan ziyara ta ganin likitocin shi, amma Annobar Korona ce ta hana shi tafiya har na fiye da tsawon shekara daya.”

Don haka yanzu zai tafi, don ganin yabi umurnin likotocin shi, kuma gwamnati na iya bakin kokarin ta na ganin ta inganta asibitocin kasar da kayan da suka dace. Garba Shehu, ya kara da cewa, sabo da irin yunkurin gwamnatin ta su, hukumar lafiya ta duniya ta yaba musu a makon da ya gabata, na irin namijin kokarin da suke yi a yaki da annobar Korona.

Masu fashin baki na kallon wannan tafiyar tasa a matsayin gazawa wajen samar da kayan aiki nagartattu don tallafawa fannin kiwon lafiyar kasar. Wanda yanzu haka kungiyar likitocin kasar ta bayyana shirinta na shiga yajin aiki a ranar Alhamis, idan har ba a biya mata bukatunta ba.

Dr. Abu Yazid, kwararren likita ne a Najeriya, wanda ya danganta irin wannan dabi’ar ta shugabannin a Najeriya ya fita kasashen ketare don samun jinya, yana ganin dalilin ba komai bane illa “rashin samar da kayan aiki na gari, hakan yasa basu da natsuwa da likitoci da kayan aiki a kasar.”

Shi kuwa talaka, ko oho, don kuwa gwamnati ba ta dauki lafiyar talakawanta da wani muhimanci ba, ya kara da cewar “Babu irin likitoci da kasashen waje je da su da babu irin su a Najeriya, don haka barnatar da dukiyar kasa ne kawai ke kai su ga irin wadanna tafiye-tafiyen masa tushe.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: