Najeriya da Chadi sun yi alkawarin durkusar da Boko Haram

0 109

Kasashen Najeriya da Chadi sun bayyana shirinsu na kawo karshen aikace-aikacen ‘yan mayakan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi ta hanyar kaddamar da sabbin tsare-tsare a yakin.  Shugaba Muhammadu Buhari da takwaransa Idris Daby, sun bayyana kaka ne bayan wata ganawar sirri da suka yi a karshen makon da ya gabata a  birnin Abuja.

Shugaba Deby na Chadi ya ce, Kasashen Tafkin Chadi da suka hada da Nijar da Kamaru da Chadi da Najeriya  za su kawo karshen rikicin Boko Haram a yankin, musamman ganin yadda suka sauya  hafsoshin tsaronsu da kuma sabon salon yakin da suka bullo da shi don murkushe tsagerun a cewarsa.

Sai dai  a yayin zantawarsa da sashen Hausa na RFI, Dr. Kabiru Adamu,  shugaban Kamfanin Bi-Com Culsultant  wanda ke nazari kan lamurran tsaro a Najeriya da yankin Sahel ya ce,

Akwai rashin yarda tsakanin kasashen Chadi da Najeriya domin kuwa ba kasafai za su amincewa  junansu ba don bai wa sojojinsu damar shiga cikin kasashensu kai tsaye ba.

Baya ga matsalar tsaro, shugabannin na Najeriya da Chadi sun sake duba dangantakar da ke tsakaninsu ta fannin bunkasar tattalin arziki, kamar yadda Ministan Hulda da Kasashen Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya tabbatar.

Shugabannin biyu sun tattauna kan batun jawo ruwa daga yankin Afrika ta tsakiya da gina hanyar mota da layin dogo daga Chadin zuwa Najeriya da kuma wutar lantarki a tsakanin kasashen biyu domin amfanin jama’armu.  

Hare-haren mayakan Boko Haram sun halaka rayukan dubban al’umma musamman a kasashen  Chadi da  Kamaru da Nijar da Najeriya, baya ga asarar miliyoyin kudade. 

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Muhammad Kabir Yusuf daga birnin Abuja

Leave a Reply

%d bloggers like this: