Duk ma’aikatan Najeriya ya kamata su zabe ni a 2023 karkashin jam’iyyar Labour Party a cewar Peter Obi

0 92

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, gabanin babban zabe mai zuwa na 2023.

Fitowarsa a matsayin dan takarar jam’iyyar ya biyo bayan nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar Labour.

Jam’iyyar ta gudanar da zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa a yau a babban birnin jihar Delta.

Wakilai 185 ne aka amince da su kada kuri’a domin zaben daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Hakanne yasa Peter Obi ya lashe biyo bayan fitowar sa a matsayin dan takara daya tilo, bayan da abokan takararsa uku suka janye masa.

Mutanen da suka  janyemasa sun hada da kwararre a fannin tattalin arziki Farfesa Pat Utomi, Olubusola Emmanuel-Tella, da kuma Faduri Joseph.

Leave a Reply

%d bloggers like this: