Fadar shugaban kasa ta gargadi jama’a da su guji yada labaran karya a shafukan sada zumunta don hana masu son raba kan Najeriya

0 85

Fadar shugaban kasa ta gargadi jama’a da su guji yada labaran karya a shafukan sada zumunta, don hana masu son raba kan kasar damar yin hakan.

Har ila yau, fadar ta yi gargadi game da mayar da martani cikin fushi, da haifar da firgici, da tabarbarewar rayuwa da asarar rayuka, da ma tashe tashen hankula biyo bayan faifan bidiyo da ake yadawa na kashe-kashen ‘yan Arewa wanda uwar kungiyar ta IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra suka yi.

Babban mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Abuja.

Hadimin shugaban kasar ya ruwaito shugaban kasa Muhammadu Buhari yana yin Allah wadai da kisan gilla da ake yi a yankin Kudu maso Gabas da ma sauran sassan kasar nan, yana mai bayyana hakan a matsayin abin damuwa.

Shugaban kasar ya gargadi wadanda suka aikata wannan aika-aika da su yi tsammanin tsatstsauran hukunci daga jami’an tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: