Labarai

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kiran da Kungiyar Dattawan Arewa ta yi wa shugaba Buhari na ya yi murabus sakamakon kalubalen tsaro

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kiran da kungiyar dattawan Arewa ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari na ya yi murabus sakamakon kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Ta ce nan ba da jimawa ba za a gudanar da sauye-sauye a harkokin tsaron kasarnan.

Babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na shugaban kasa, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja, ya ce murabus din shugaban kasar ba zai taba zama mafita ga matsalolin tsaron kasarnan ba.

Ya bayyana cewa tuni hukumomin tsaro suka kara zage damtse wajen magance yawaitar hare-haren ta’addanci na ‘yan kwanakinan, musamman a jihohin Kaduna da Neja da kuma yankin Neja Delta, bisa ga umarnin shugaban kasa.

A cewarsa, dakarun tsaro sun samar da sabon tsari bisa ayyukan da ake gudanarwa a yankunan da abin ya shafa domin samun sakamako mai kyau.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: