Majalisar Zartarwa ta amince da Naira miliyan dubu 1 da miliyan 400 domin siyan karin kayan aiki ga Kamfanin Watsa Wutar Lantarki na kasa

0 58

Majalisar Zartarwa ta Tarayya a jiya ta amince da Naira miliyan dubu 1 da miliyan 400 domin siyan karin kayan aiki ga Kamfanin Watsa Wutar Lantarki na kasa, a wani bangare na kokarin inganta wutar lantarki a kasarnan.

Amincewar ta zo ne kasa da mako guda bayan da kasarnan ta fuskanci rugujewar tsarin wutar lantarki karo na biyar a cikin watanni uku.

Ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labaran fadar shugaban kasa a karshen taron da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ya ce an amince da kudin kwangilar da tashar wuta da ke Kafanchan a jihar Kaduna, tare da fadada layin wuta a tashar Jos ta jihar Filato. Ya ce ayyukan za su ci kudi kimanin naira miliyan 132 da dubu 700.

Amincewa ta biyu da ya samu ita ce samar da kayan aiki da motocin aiki ga Kamfanin Watsa Wutar Lantarki na kasa akan kudi naira miliyan dubu 1 da miliyan 300.

Leave a Reply

%d bloggers like this: