Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar wa tubabbun mayakan Boko Haram goyon bayan gwamnatin Najeriya

0 89

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar wa tubabbun mayakan Boko Haram goyon bayan gwamnatin tarayya tare da sama musu halaltacciyar hanyar samun kudin shiga don fara sabuwar rayuwa.

Mayakan da suka mika wuya sun yi wa Osinbajo kyakkyawar tarba a lokacin da ya ziyarce su a Hajji Camp da ke Maiduguri a jiya a wata ziyarar aiki da ya kai jihar.

Tun da farko a fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, a lokacin da ya raka mataimakin shugaban kasa, gwamnan jihar, Babagana Zulum, ya roki gwamnatin tarayya da ta tallafawa kokarin gwamnatin jihar na sake tsugunar da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu na asali.

Ya kuma jadadda cewa akwai bukatar a kula da masu tada kayar bayan da suka mika wuya.

Gwamnan ya kara da cewa jihar Borno tana da ‘yan asalin jihar kimanin dubu 66 da ke zaune a jamhuriyar Kamaru, da mutane dubu 120 a jamhuriyar Nijar kuma kimanin dubu 25 da ke zaune a jamhuriyar Chadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: