Fasinjojin 9 sun rasu bayan motar su ta fada cikin Dam din da ke kan hanyar Kano zuwa Katsina a karamar hukumar Gwarzo ta Jihar Kano

0 82

Kimanin Fasinjojin wata Mota 9 ne suka rasu bayan Motar su ta fada cikin Dam din Fada wanda ya ke kan hanyar Kano zuwa Katsina a karamar hukumar Gwarzo ta Jihar Kano.

An bada rahotan cewa daga cikin Fasinjojin Mota 12, an yi nasarar ceto 3 daga cikin su a raye.

Kakakin Hukumar Kashe Gobata ta Jihar Kano Mallam Saminu Yusif, shine ya bada tabbacin faruwar lamarin, inda ya ce hadarin ya faru da Mota kirar Golf Wagon wanda ta dauko Fasinjojin 12 wanda ta taso daga Kano zuwa Katsina.

A cewarsa, hukumar su ta samu kirar gaggawa daga wurin wani mai suna Ali Mai Faci, wanda ya sanar da faruwar lamarin a Dam din Fada da ke Gwarzo.

Sanarwar ta ce bayan Jami’an su na Ofishin Hukumar na Gwarzo sun garzaya wurin sun tsinci motar a cikin Dam din.

Haka kuma ya ce Jami’an nasu, sun yi nasarar fitar da Gawarwakin mutane 9 da kuma wasu Rayayyu 3.

Leave a Reply

%d bloggers like this: