Gabatar da takardin bogi ne yasa muka kwace takarar Aminu Kanta – Kotu

0 90

Wata Kotun Tarayya ta Soke Halascin Zaben Hon Aminu Kanta Babura, a matsayin Dan Takarar Majalisar Tarayya Mai wakiltar na Jam’iyar APC a Jihar Jigawa.

Kotun a hukuncin da ta yanke a yau, ta bayyana Hon Aminu AK Babura na Jam’iyar APC, a matsayin mutumin da bai cancanci tsayawa takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Babura da Garki ba.

Haka kuma Kotun, ta ayyana Alhaji Isa Dogonyaro, a matsayin halastaccen dan Takarar Jam’iyar APC mai wakiltar Mazabun biyu a Jihar Jigawa.

Alkalin Kotun, Mai Sharia Emeka Nwite, ya umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta sauya sunan Aminu Kanta Babura, da sunan Hon Isah Dogonyaro, a matsayin wanda zai yiwa Jam’iyar APC takara Majalisar Tarayya mai wakiltar Babura da Garki a zaben shekarar 2023.

Kotun ta amince da bukatar da Barista Sunusi Musa, Lauyan Alhaji Isah Dogonyaro ya gabatar mata na cewa Aminu Kanta, ya karya ka’idojin Sashe na 66 (1) (i) na kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 da kuma Sashe na 29 (5) da (6) na Dokokin Hukumar Zabe na shekarar 2022 da muke ciki.

Manema Labarai sun rawaito cewa ana zargin Aminu Kanta AK, da gabatar da bayanan karya kan Makarantar da ya yi Firamare a  Takardun da ya gabatarwa da hukumar INEC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: