Yan Civil Defence ta yi nasarar kama wani mutum mai shekaru 75 da laifin yiwa wata Jikar-Jikarsa yar shekara 6 fyade a Malam Madori

0 103

Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Kasa reshen Jihar Jigawa ta yi nasarar kama wani mutum mai suna Musa Gambo, dan shekara 75 da laifin yiwa wata Jikar-Jikarsa yar shekara 6 a Duniya fyade.

Kakakin rundunar na Jiha CSC Adamu Shehu, shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse.

A cewarsa, an kama mutumin ne a lokacin da wata Ma’aikaciyar Al’ummar ta samu kirar gaggawa daga wurin Iyalin Yarinyar wanda suka kama shi a hannu a lokacin da ya ke aikata aika-aikar da Yarinyar wanda ta kaiwa Kakarta Ziyara.

CSC Adamu Shehu, ya ce an kama tsohon ne a makon da ya gabata a unguwar Gandun Sarki na karamar hukumar Malam Madori, bisa laifin yiwa yarinya yar shekara 6 fyade.

Sanarwar ta ce wata mata mai suna Malama Maimuna ce ta kama mutumin tare da Yarinyar a lokacin da yake lalata da ita a dakin sa.

Haka kuma ya ce yarinyar ta fadawa Jami’an tsaro cewa mutumin ya jima yana yin lalata da ita, inda ya ke bata Alawowi da kuma barazanar kashe ta matukar ta fadawa wani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: