Fira Ministan Pakistan Imran Khan ya rasa matsayinsa bayan ya sha kaye a zaben majalisar dokokin kasa

0 33

Fira Ministan Pakistan Imran Khan ya rasa matsayinsa a lahadin nan, bayan da ya sha kaye a zaben majalisar dokokin kasar ta Pakistan.

An dai sauke Imran Khan ne, bayan shafe makwanni ana rikicin siyasa a kasar Pakistan.

Mukaddashin kakakin majalisar kasar Sardar Ayaz Sadiq ya ce ‘yan majalisa 174 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudirin yankan kauna kan jagorancin tsohon Fira Minista Imran Khan.

Babu wani Fira Minista da ya taba yin cikakken wa’adi a Pakistan, amma Khan shi ne na farko da ya rasa mukaminsa ta hanyar kada kuri’ar rashin gamsuwa da gwamnatinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: