Yau ake gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Katsina

0 94

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Katsina (KATSIEC) ta fara rabon muhimman kayayyakin zabe ga kananan hukumomin jihar 34 gabanin zaben kananan hukumomin jihar da za a yi gobe Litinin.

Da yake zantawa da manema labarai yayin da yake mika kayan zaben a babban bankin Najeriya reshen Katsina, shugaban hukumar, Alhaji Ibrahim Bako, ya ce kayayyakin za su isa kananan hukumomin ne a yau Lahadi domin raba wa mazabu da rumfunan zabe a safiyar ranar Litinin.

Ya kara da cewa muhimman kayan aikin sun hada da katunan zabe, tawada da kuma takardar sakamako, yayin da tuni duk sauran kayayyakin aka aike da su.

Shugaban hukumar ya ce sama da ma’aikatan wucin gadi 9,000 ne za su gudanar da zaben da sama da mutane miliyan uku da suka yi rajista a jihar.

Ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa 12 ne za su shiga zaben a fafata.

Daga nan sai Alhaji Bako ya bukaci jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa su kasance masu gudanar da ayyukansu cikin lumana tare da bin ka’idojin zabe kamar yadda dokar zabe da akayiwa gyara a 2010 ta tanada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: