Firaministan Birtaniya Keir Starmer Ya Bukaci Turai Ta Rage Dogaro da Amurka

0 239

Firaministan Ƙasar Birtaniya, Keir Starmer, ya bukaci ƙasashen Turai su rage yawan dogaro da Amurka wajen harkokin tsaro.

Da yake jawabi a taron tsaro na Munich, Starmer ya ce dole ne Turai ta ƙarfafa haɗin kai da kuma gina nata ƙarfin tsaron domin kare kanta daga barazanar duniya.

Ya jaddada cewa babu cikakken tsaro ga Birtaniya ba tare da Turai ba, haka kuma babu tsaron Turai ba tare da Birtaniya ba, yana mai cewa tarihi ya tabbatar da hakan.

Starmer ya amince cewa Amurka abokiya ce, amma ya ce lokaci ya yi da Turai za ta ƙara ɗaukar nauyin kare kanta tare da gina ƙarfin soji mai zaman kansa.

Firaministan ya kuma nuna damuwa kan yadda masana’antar tsaron Turai ke rarrabe, yana mai cewa hakan na rage inganci da jawo maimaita ayyuka ba tare da amfani ba.

Ya bayyana Turai a matsayin “babbar giwa mai barci”, yana mai cewa tattalin arzikin Turai ya fi na Rasha ƙarfi sosai.

A ƙarshe, Starmer ya yi kira ga ƙasashen Turai su haɗa kai, su ɗauki alhakin tsaron kansu, domin tabbatar da kare dimokuraɗiyya, ’yanci da kuma makomar al’ummarsu.

Leave a Reply