Jiragen Sojin Amurka Sun Sauka A Maiduguri Domin Tallafawa Tsaro A Najerya

0 225

Jiragen saman sojin Amurka sun fara sauka a sansanin sojin sama da ke Maiduguri, yayin da ake shirin fara tura dakarun Amurka zuwa wasu sassan Najeriya domin bayar da tallafin fasaha da shawarwari kan harkokin tsaro.

Wani jami’in ma’aikatar tsaron Amurka, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda yanayin aikin, ya shaida cewa jiragen da suka isa Maiduguri su ne na farko cikin jerin jiragen C-17 da ake sa ran za su rika sauka a wurare uku masu muhimmanci a Najeriya cikin makonni masu zuwa.

Jami’an tsaro sun bayyana cewa zuwan farkon zai fi mayar da hankali ne kan kafa hanyoyin sadarwa, gine-ginen sansani da kuma tsarin tallafin aiki tare da hadin gwiwar sojojin Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya jaddada cewa dakarun Amurka ba za su shiga artabu ba. Ya ce sojojin Najeriya ne za su ci gaba da rike cikakken iko da dukkanin ayyukan tsaro da kuma jagorantar duk wata manufa a cikin ƙasar.

Ya kuma bayyana cewa tura dakarun ya biyo bayan shawarwarin kwamitin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya, kuma manufar ita ce bayar da shawarwari da taimakon fasaha kawai, ba shiga yaki ba.

A cewar jami’an Amurka, ana sa ran ci gaba da saukar jirage cikin makonni masu zuwa a matsayin wani bangare na aiki na wucin gadi domin tallafawa yaki da ta’addanci. Sabbin dakarun za su kara karfafa karamin rukunin masu ba da shawara na Amurka da tuni suke aiki a Najeriya, musamman wajen tsara tsare-tsare da musayar bayanan sirri.

Wannan mataki na zuwa ne mako guda bayan zirga-zirgar jiragen sojin Amurka a yankin Afirka ta Yamma. Bayanai daga masu bibiyar zirga-zirgar jiragen sama sun nuna cewa jiragen daukar kaya shida sun sauka a yankin tsakanin 6 zuwa 14 ga watan Fabrairu, inda mafi yawansu suka ratsa Accra a Ghana kafin su karasa sansanonin sojin sama na Najeriya, musamman Maiduguri, wadda ake hasashen za ta zama babbar cibiyar gudanar da ayyukan tallafi kan yaki da ISWAP a jihar Borno.

Leave a Reply