Fitattun Shirye-Shiryen Sawaba Dake Burge Masu Saurare

3 210

Bayan fara yada shirye-shiryen Gidan Radio Sawaba, Mutane da dama sun nuna sha’awarsu tare da fatan alheri ga kafar sadarwar sakamakon farin jinin da ta samu cikin lokaci kadan a dalilin managartan shirye-shiryen da take gabatarwa. Daga cikin Shirye-shiryen da masu sauraren ke zumudinji sun hadar da;

Nazaune- Shiri ne da ya shafi labaran abubuwan ban al’ajabi, ban mamaki, ban haushi da kuma ban dariya.

Duniya mata- Shiri ne na musamman akan al’amuran da suka shafi zamantakewar rayuwar mata da irin kalubalen da suke fuskanta a gidajen aurensu da hanyoyin da za a bi domin magance matsalar.

Haka nan shirin ya kan haskaka rayuwar wasu daga cikin matan da suka yi fice a harkokin rayuwarmu ta  yau da kullum.

Turmin danya- Shiri ne da ke ba wa ‘yan siyasa damar bajekolin ra’ayoyinsu karkashin sahi na 39 na kundin tsarin mulkin kasa na fadin albarkacin baki ya bada dama.

Mu Zagaya Duniya – Shiri ne dake Hawa Jirgi Tare da mau saurare domin zagaya wa da su kasashen duniya dake nahiyoyi daban-daban a Duniya domin gano yadda suke tafiyar da zaman takewar rayuwarsa.

Labarun Duniya- Mukan kawowa masu saurare Labarun da suka shafi Jihar Jigawa, Arewa Maso Yammacin tare da labarun sauran sassan Kasa baki daya. Hakan ta sanya jama’a ke mararin sauraren labarun Sawaba a koda yaushe.

Sawaba FM na cigaba da zage damtse don kawo muku shirye-shiryen da zasu Nishadantar da ku gami da Fadakarwa a Koda Yaushe.

Haka Zalika Muna maraba da shawarwarinku masu bibiyarmu domin don ku muke shirye-shiryenmu.

 1. malam_fari says

  Ina jindadin dukkan shirye_shiryenku musanman Wanda kuke gayyato manyan baki masana kamar a bangaren noma da kuma shirin turmin danya

 2. malam_fari says

  Shawara ta ga Sawaba Fm itace inaso wadansu daga cikin ma’aikatansu su dan rage saurin fushi yayin da suke amsa wayoyin masu saurare.
  Muma masu saurare munajin babu dadi idan mai kiran waya yayi wani abinda ba Dai_Dai ba.
  Toh amma bai kamata su nunawa duniya cewar abin bai musu dadi a take a wajen ba kasancewarsu masu kawo gyara cikin al’umma kamata yayi ace sunyi amfani da salon fikira wajen ganin wani mutumin bai sake maimaita wannan laifin ba

  Nagode

  1. Sawaba FM says

   Muna Godiya da wannan shawara taka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: