Makasudin Kafa Gidan Radio Sawaba FM 104.9

2 388

Radio Sawaba na yada shirye-shirye akan 104.9 Mhz zangon FM dake kan titin Garun Gabas cikin garin Hadejia a jihar Jigawa.

Ta fara watsa shirye shirye ne kai tsaye a ranar 9 ga watan Afrilu 2019, shiri na farko da aka fara gabatarwa shi ne labaran duniya cikin Harshen Hausa da misalin karfe 6:30 na safe agogon Najeriya.

Manufar kafa gidan radio Sawaba ita ce wayar da kan al’ummar jihar Jigawa tare da ilmantar da su ta hanyar shirye-shiryen da suka shafi rayuwarsu ta yau da kullum.

Jihohi da dama sun sami cigaba ta hanyar samuwar gidajen radio da talabijin, amma a jihar Jigawa akwai karancin kafafen yada labarai, wannan ta sa aka kirkiro da Sawaba FM domin ta canja tunanin al’umma daga hanya maras kyau zuwa hanya madaidaiciya.

Haka nan Sawaba ta zo ne domin samarwa da alumma sauki daga cikin halin kunci na rayuwa da suke ciki, ta hanyar wayar musu da kai wajen Gudanar da sana’oin dogaro da kai.

KADAN DAGA CIKIN SHIRYE SHIRYEN SAWABA FM;

 1. Labaran Duniya
 2. Sharhin jaridu
 3. Duniyar wasanni
 4. Duniyar mata
 5. Jigawa tarin Allah
 6. Fasahar noma
 7. Nazaune bai ga gari ba
 8. Turmin danya
 9. Najeriya a yau
 1. malam_fari says

  Muna maraba da dukkanin shirye_shiryenku #sawaba_radio_fitilar_rayuwa
  Tabbas mun fara ganin chanji

 2. hassan Muhammad inuwa hadejia says

  babushakka muna farinciki dasamun wannan gidana radio mai albarka dafatan Allah yasa yazamto alkhairi ga alummar hadejia jigawa dama Nigeria baki daya Sawaba radio fitilar rayuwa

Leave a Reply

%d bloggers like this: