Ambaliyar ruwa ta janyo zabtarewar kasa a arewa maso gabashin jihar Assam da ke Indiya, tare da hallaka mutum 25, wasu 65,000 kuma suka tsere daga gidajensu.

A ranar Talata ne jami’ai a jihar suka ce kwanaki goma ke nan ana tafka ruwan sama mai karfin gaske, kuma da ma can jihar Assam na fama da mamakon ruwan sama a duk shekara dalilin da ya sa mutane ke barin muhallansu tun kafin damuna ta kankama.

Shi ma kogin Brahmaputra, daya daga cikin mafi girma a duniya, da ya taso tun daga Tibet ya dangana da Indiya, ya kuma ratsa Bangladesh, ya yi ambaliya har kogin jihar Assam, tare da ratsawa kauyuka1,800 a gundumomi 26 cikin wannan watan kadai.

Hukumomi jihar sun ce, ambaliyar ta ta kuma shafi tashoshin jiragen kasa da ke yankin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: