Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar Jigawa ta yi barazanar daukar mataki akan wanda aka samu da laifin cin iyakar makiyaya

0 81

Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar Jigawa ta yi barazanar daukar mataki akan wanda aka samu da laifin cin iyakar makiyaya tare da kutse a dajin gwamna da kuma sare bishiya ba bisa ka’ida ba.

Kwamishinan ma’aikatar, Alhaji Ibrahim Baba Chaichai, ya yi wannan gargadi lokacin da ya ziyarci garuruwan Kwari da Safa da Kumbura da ke gundumar hakimin Sundumina a karamar hukumar Birnin kudu.

Ibrahim Baba Chaichai wanda ya yi wannan gargadi ta bakin darakta mai kula da sashen gandun daji da rainon bishiyoyi na ma’aikatar, Alhaji Yahaya Uba Kafin Gana, ya nuna damuwa bisa yadda wasu batagari a garuruwan uku su kai kutse a dajin gwamna suka mayar da su gonaki.

Ya bukaci batagarin dasu hanzarta ficewa daga dajin in kuma sun ki bin wannan umarni to kuwa doka za ta hau kan su.

Kwamishinan ya kuma gargadi dukkan masu aikata hakan a fadin jiharnan da su yiwa kansu kiyamul laili, domin duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: