Yadda Ibrahim Saminu Turaki ya kasance dan takarar sanata mai wakiltar mazabar Jigawa ta Arewa maso Yamma – PDP

0 103

A jiya ne aka zabi tsohon gwamnan jihar Jigawa, Ibrahim Saminu Turaki a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar Jigawa ta arewa maso yamma.

Saminu Turaki wanda ya koma jam’iyyar PDP kwanan nan ya ci zabe babu hamayya a zaben da ya gudana a karamar hukumar Gumel.

Haka kuma, an zabi Hussaini Namadi a matsayin dan takarar sanatan Jigawa ta arewa maso gabas a jam’iyyar ta PDP, sai Mustapha Habib a Jigawa ta kudu maso yamma, ba tare da hamayya ba.

Hussaini Namadi ya wakilci mazabar tarayya ta Hadejia/Auto/Kafin-Hausa a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015 yayin da Mustapha Habib ya wakilci mazabar tarayya ta Miga/Jahun a majalisar wakilai.

Zaben nasu ya gudana ne a hedkwatar Sanatan Hadejia da Dutse.

Jami’ai daga hedikwatar jam’iyyar ta kasa da kuma jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ne suka sanya ido a zabukan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: