Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023

0 90

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, a jiya ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023.

Habu Zarma, wanda shi ne jami’i mai kula da zaben, ya ce Dankwambo ya samu tikitin ne biyo bayan janyewar sauran ‘yan takara biyu, tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Usman Bayero Nafada, da wani dan kasuwa, Hamma Saleh.

An gudanar da zaben fidda gwanin ne a gundumar sanatan Gombe ta Arewa, a karamar hukumar Malam-Sidi Kwami.

A wani labarin na siyasa, Sarkin Damaturu a jihar Yobe, Hashimi El-Kanemi, ya ce masarautarsa za ta goyi bayan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo tare da yin addu’a domin Allah ya sa ya zama shugaban kasa a 2023.

Sarkin ya yi wannan alkawarin ne a jiya a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin shugaban kasar da ya kai ziyarar ban girma a fadarsa da ke Damaturu.

Yemi Osinbajo ya je jihar Yobe ne a cigaba da tuntubar da yake yiwa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: