Labarai

Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari

Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari a karshen mako.

Shaidu sun ce ‘yan bindiga ne a kan babura suka yi wa mutanen garin luguden wuta a lokacin da suka shiga daji domin dibar itace.

A cewar shaidun, wasu da dama da lamarin ya rutsa da su sun tsira da raunukan harbin bindiga.

Ana fargabar cewa an sace ko kashe wasu da dama a lamarin.

Har yanzu dai ba a san ko su waye suka kai harin ba, amma kungiyoyin Boko Haram da ISWAP na ci gaba da kaddamar da yakin tada kayar baya a yankin.

Har yanzu dai jami’an tsaro ba su ce uffan ba game da harin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: