Shugaban gidauniyar Abdullahi Mahmood (AMF) ya kaddamar da wani muhimmin shirin tallafawa dalibai a karamar hukumar Mallam-Madori.
Shirin, wanda aka kaddamar a ranar litinin data gata, yana da nufin karfafa halartar dalibai a kowace rana, da tallafa wa ilimin ‘ya’yan mata, kiwon lafiya, da kuma nuna kyawawan dabi’u a tsakanin dalibai.
Za’a aiwatar da shirin ciyarwa a dukkan mazabu da kauyuka da ke Mallam-Madori da kewaye, baya ga dalibai, shirin zai hada da malamai, iyaye, shugabannin al’umma da na addini, domin fadakar da jama’a kan muhimmancin ilimi da illolin ta’ammali da miyagun kwayoyi, da kuma inganta zaman lafiya da hadin kai.
Haka kuma, shirin zai tallafawa manufofin ilimi da ci gaban al’umma da gwamnatin jihar Jigawa ke aiwatarwa.