Manoman shinkafa dubu biyar ne zasu shiga shirin noman shinkafa ‘yar rani a jihar Jigawa

0 540

Mai baiwa gwamna shawara kan shirin noma Dan Riba Muhammad Idris Danzomo ne ya sanar da hakan ta cikin shirin radio na Jigawa  A Yau.

Ya ce an bullo da shirin ne domin habaka noman shinkafa kasancewar Jigawa ce jiha ta farko ko kuma ta biyu a noman shinkafa a fadin kasar nan.

Muhammad Idris Danzomo yana mai cewar a jihar Jigawa ana noma sau uku, lokacin Rani da tsakiyar rani da da kuma lokacin damina.

Ya cigaba da cewar hakan zai hana matasa zuwa kudu domin yin ci rani, kuma hakan yana mayar da matasa miliyoyi ta hanyar noman shinkafa

Mai baiwa gwamnan shawara ya kuma ce za’a baiwa manoma kashi biyar bashin noman shinkafa ‘yar Rani da zasu biya bayan sun yi girbi. Ya bukaci manoman shinkafa da su shigo a dama dasu, wajen bunkasa noman shinkafa a jihar nan, inda ya ce an yi amfani da malaman gona wajen tattara manoma rukuni-rukuni domin amfana da shirin.

Leave a Reply