Gwamnonin jam’iyyar APC sun bayyana jin daɗinsu bisa cigaban da aka samu a cikin shekaru biyu da suka gabata a Jihar Jigawa.
Darakta Janar na kungiyar Mr Folarinsho Aluko ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ziyarar ban girma ga Gwamna Umar Namadi a ofishinsa
Ya bayyana cewa ziyarar ta kasance wani ɓangare na yawan gani da ido da manema labarai a jihohin da jam’iyyar APC ke mulki.
Babban Daraktan ya ƙara da cewa wannan ziyara za ta ba su damar samun karin bayani kan aiyukan da aka kammala domin karfafa musayar ra’ayi tsakanin gwamnonin APC.
Ya nuna farin ciki da irin tarbar da aka yi musu tun bayan zuwansu jihar. A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya yaba wa zauren bisa wannan ziyara a madadin Gwamnatin Jihar da al’ummarta, inda ya ce hakan zai taimaka wajen wayar da kan jama’a kan manufofin gwamnatin sa guda goma sha biyu da aka tsara domin ciyar da jihar Jigawa gaba.