Gidauniyar kamfanin NNPC ta kaddamar da tiyatar Yanar Ido kyauta ga mutane 300 a jihar Jigawa

0 129

Gidauniyar kamfanin man fetir ta kasa NNPC bisa sahalewar gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da shirin yiwa mutane 300 aikin tiyatar Yanar Ido kyauta a jihar Jigawa

Daya daga cikin jamian gudanar da aikin kuma Kwararren Likitan Ido a maaikatar lafiya ta jiha Dr Abdullahi Idris ya sanar da hakan ga manema labarai a babban asibitin Dutse

Ya ce gidauniyar zata baiwa masu matsalar ido dubu uku magani kyauta a shiyyar arewa maso yamma yayinda a jihar Jigawa za a yiwa mutane 300 aikin tiyatar Ido kyauta

Dr Abdullahi Idris yana mai cewar an fara aikin tiyatar Idon ne kyauta daga ranar laraba 30 ga watan Mayu zuwa Talata ta makon gobe

A cewarsa an duba mararsa lafiyar ido da dama tare da raba magani ga masu matsalar ido dubu daya a jihar Jigawa

Dr Abdullahi Idiris kuma shugaban kwamitin harkokin Ido na maaikatar lafiya ta jiha ya ce a yanzu haka sun kammala tantance masu matsalar ido fiye da dari uku da za a yiwa aikin tiyatar kyauta a jihar Jigawa

A jawabansu daban daban wadanda suka amfana da aikin sun yabawa gidauniyar bisa wannan karamci

Leave a Reply