Gomman mutane sun tsere daga jihar Zamfara bayan wani harin ƴan fashin daji

0 167

Gomman mutane sun tsere daga kauyen ‘Yan Buki cikin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, bayan wani harin ‘yan fashin daji.

An bayar da rahoton kisan mutane 7 tare da sace wasu a yayin harin da aka kai kauyen jiya da rana.

Da yake zantawa da BBC Hausa, wani mazaunin kauyen da ba a ambaci sunansa ba, yace ‘yan fashin dajin sun mamaye kauyen da tsakar rana.

Ya kara da cewa ‘yan fashin sun kuma cinnawa shaguna wuta tare da kone kayan abinci a rumbuna.

Mutumin yace dukkan mutanen kauyen da suka rage, sun samu tserewa tare da shiga motar da ta kai su birnin Gusau.

Sai dai kawo yanzu ‘Yan sanda ba su tabbatar da wannan harin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: