Gwamna Badaru Abubakar ya ce akwai yiwuwar sake ƙaƙaba dokar hana zirga-zirga a jihar Jigawa saboda cutar Corona

0 207

Da yake nuna damuwa kan rahotannin tafiyar hawainiya na allurar rigakafin cutar corona a jiharnan, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ya ce akwai yiwuwar sake kakaba dokar hana zirga-zirga a Jigawa.

Gwamnan, wanda damuwarsa ta bayyana a fuskarsa, ya sanar da hakan ne yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da gangamin rigakafin corona da aka gudanar a karamar hukumar Kiyawa.

Bayanai sun nuna cewa yayin da mutane dubu 122 da 200 aka yiwa allurar rigakafin farko a jihar, mutane dubu 53 da 753 ne kawai aka yiwa allurar rigakafin karo na biyu a fadin jihar.

Gwamnan wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a lamunta ba, ya kuma sha alwashin yin tir da duk wani yunkuri na mayar da jihar Jigawa kasar Sifaniya.

da sauran kasashen ketare inda annobar cutar ta sake bulla a sakamakon sakacin da jama’a ke yi.

Gwamna Badaru wanda ya tabbatarwa al’umma lafiya da ingancin rigakafin, ya ce ba zai amince da duk wani abu da zai jefa rayuwar al’ummarsa cikin hadari ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: